Barcelona da Bayern: Ba ƴan kallo za a buga wasa tsakanin ƙungiyoyin—BBC Hausa

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Robert Lewandowski

Bayern Munich za ta karɓi baƙwancin Barcelona inda za a buga wasan ba tare da ƴan kallo ba a gasar Champions League a ranar 8 ga watan Disamba a daidai lokacin da ake samun ƙaruwa a adadin masu kamuwa da korona a Bavaria.

A farkon wannan makon ne Shugaban Bavaria, Markus Soder ya bayyana cewa akwai yiwuwar a ɗauki irin wannan matakin, inda ya ce “ƙwallon ƙafa na da rawar da take takawa matuƙa”.

Bayern Munich ta samu nasara a matakin sili ɗaya ƙwale inda ta zama zakara a rukunin E, da kuma karawa tsakanin Barcelona da kuma Benfica domin zuwa mataki na biyu a cikin 16 na ƙarshe.

Barcelona za ta je gaba muddin ta samu nasara.

Sai dai idan aka yi kunnen doki ko kuma aka doke ta, hakan zai ba Benfica nasara a matakin sili ɗaya ƙwale gabannin Barcelona da nasara a ɓangaren Dynamo Kiev.

An ci Barcelona 3-0 a wasanta da Bayern a Nou Camp a watan Satumba, haka kuma zuwan su na ƙarshe zuwa Allianz Arena an ta shi 3-2 a zagayen kusa da na ƙarshe a wasan zagaye na biyu da suka buga a Maris ɗin 2015.

Sai dai Barcelona ta wuce zuwa wasan ƙarshe sakamakon nasarar da ta samu ta 3-0 inda ta doke Juventus a wasan ƙarshe wanda hakan ya sa ta ɗauki kofin Champions League na biyar kuma shi ne na baya-bayan nan.

More News

Sabon gwamnan Taraba ya tsige kantomomin ƙananan hukumomi

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya amince da rusa kwamitin riko na kananan hukumomi goma sha shida na jihar nan take. Rushewar wanda ke kunshe...

Abba Kabir ya kori shugaban hukumar jin dadin alhazan Kano

Kasa da sa’o’i 24 da hawan kujerar shugabancin jihar Kano, da sanyin safiyar Talatar nan ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kori...

Yadda Buhari ya isa Daura bayan zamowa tsohon shugaban Najeriya

A yau Litinin ne shugaba Buhari ya isa mahaifarsa ta Daura bayan mika mulki ga Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Tinubu dai ya zama shugaban...