Manchester United na kara samun kwarin gwiwar a yunkurin da take yi na sayo dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund a bazara. (Standard)
Barcelona na son dauko Lautaro Martinez, mai shekara 22, daga Inter Milan amma suna sane cewa za su fuskanci kalubale daga Real Madrid da Manchester City wajen sayo dan wasan na Argentina (Marca)
Wolves ba za ta sayar da Adama Troare kasa da £70m a bazara ba bayan da ake rade radin cewa dan wasan na Spaniya mai shekara 24 zai koma Liverpool. (Football Insider)
Arsenal ta sanya ido kan dan wasan Athletic Bilbao Unai Nunez wanda take son daukowa lokacin musayar ‘yan kwallo. Za a sayar da dan wasan na Spaniya mai shekara 23 a kan euro 30m. (La Razon – in Spanish)
- Coronavirus ta kashe mahaifiyar Pep Guardiola
- Real Madrid na zawarcin Harry Kane
Hukumar kwallon kafar duniya, Fifa, na shirin tsawaita kakar wasa ta 2019-20 zuwa abin da hali ya yi domin bai wa tawagar ko wacce kasa damar yanke shawara kan lokacin da za ta kammala kakar wasanta. (The Athletic – subscription required)
Liverpool, Manchester City da kuma Manchester United dukkansu sun bukaci a gaya musu lokacin da Valencia za ta sanya dan wasan Spaniya mai shekara 20 Ferran Torres a kasuwa. . (Goal)
Dan wasan Manchester United Jesse Lingard, mai shekara 27, ba shi da niyyar barin kungiyar a bazara. A baya an yi rade radin cewa dan wasan na kasar Ingila zai koma ko dai Arsenal ko kuma Everton(Metro)
Liverpool na duba yiwuwar soma zawarcin dan wasan Switzerland Denis Zakaria da takwaransa na Faransa Marcus Thuram daga Borussia Monchengladbach.(Express)
Dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, ya soma tattaunawa da Chelsea a kan sabunta kwantaraginsa a Stamford Bridge(Football.London)
Chelsea na shirin yin gogayya da Arsenal wajen dauko dan wasan Jamus Jerome Boateng, wanda ke shirin soma wata 12 na karshe na kwangilarsa a Bayern Munich. (Mail)