Barayi sun kwashe wa Dele Alli gwala-gwalai

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alli ya buga wa tawagar Ingila a gasar kofin duniya

has 37 England caps and was part of his country’s squad at the 2018 World Cup in Russia

‘Yan fashi rike da wuka sun shiga gidan dan kwallon Tottenham, Dele Alli inda suka kwashe masa dukiya.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da asuba, inda mutum biyu maza suka shiga gidan dan kwallon Ingilar a yankin arewacin London.

Barayin sun yi wa Alli barazana da wuka sannan suka nushe shi – a yayin da ya ji rauni a fuskarsa.

Barayin sun yi awon gaba da gwala-gwalai kafin su tsere.

A halin yanzu dai, Alli ya mika wa ‘yan sanda bidiyon CCTV na lamarin.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...