Bankin Raya Kasashen Musulmi Zai Gina Asibiti Mai Gado 300 A Kaduna

Bankin raya kasashen musulmi ya shirya gina asibiti mai gado 300 a jihar Kaduna.

Shugaban bankin ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da suka yi da ministar kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmad a Abuja.

Shugaban bankin, Muhammed Al Jasser shi ne ya bayyana haka bayan ganawar ta su da ministan cikin wani sako da ya wallafa a shafin bankin na Twitter.

Al Jasser ya ce za a samar da asibitin karkashin tsarin yarjejeniyar Murabaha.

Ya kara da cewa wannan wani bangare na taimakawa fannin kiwon lafiya a Najeriya.

More from this stream

Recomended