Bankin kasar China ya bada bashin kuɗin aikin layin dogo daga Kano-Kaduna

Bankin Samar da Cigaba na ƙasar China wato China Development Bank(CDB) ya amince da bayar da bashin dala miliyan $254.76 domin gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna.

A wata sanarwa ranar Talata bankin ya ce ana sa ran kuɗin zai taimaka wajen cigaba da yin aikin na samar da abun more rayuwa.

Bankin ya ce kamfanin gine-gine na China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) shi ne ke gudanar da aikin samar da layin dogon.

Aikin layin dogo na zamani daga Kano-Kaduna na da nisan kilomita 203.

Da zarar an kammala aikin zai haɗe da layin dogo da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja.

A shekarar 2021 ne tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya kaddamar da fara aikin a wani biki da aka gudanar a garin Kano.

More from this stream

Recomended