An zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.
Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban kungiyar.
Muhammed da Fubara an zaɓe su ne a ranar Asabar a wurin wani taron sanin makamar aiki da aka yi wa waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyar PDP da aka gudanar a Bauchi.
Da yake magana a wurin taron shugaban riko na jam’iyyar PDP, Umar Damagum ya shawarci mambobin da su haɗa kai suyi aiki tare a matsayin ƴan uwa.
Muhammed zai maye gurbin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde wanda ya zama mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.