Babu wanda ya isa ya kamani, ina aikin Allah ne – AREWA News

0

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya cika baki a wani sabon fefan bidiyo cewa baza a iya kama shi ba saboda yana aikin Allah kuma Shi zai cigaba da kare shi.

“Babu wanda ya isa ya kamani saboda ina aikin Allah ne. Shi zai kare ni kamar yadda yake kare masu aiki makamancin haka kuma suke neman kariyarsa,” Shekau ya fada a cikin wani fefan bidiyo na tsawon mintuna 30 da ya fitar a matsayin martani kan farautarsa da rundunar sojan Najeriya ta fara da shi da manyan kwamandodinsa.

“Ina da tabbacin Allah zai kare kwamandodi na.Dukkaninmu muna aikin Allah ne.”

A cikin fefan bidiyon anga Shekau yans zaune kewaye da mayakansa guda biyu a cikin wani karamin daki da bashi da fadi.

A ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba ne rundunar sojan Najeriya ta sake fara sabuwar farautar Shekau tare da kwamandodinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here