Babu mai iya ja da Buhari a zaben 2019, inji El-Rufai -#BBCNigeria2019

Nasir El-Rufai, Gwamnan jihar Kaduna, ya bayyana cewa ba a taba dan siyasa ko ma’aikacin gwamnati da talakawa suka yarda da shi a Najeriya ba kamar Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya ce ‘yan kasar sun san tarihin shugaban bai taba cin amana a ayyukan da ya gudanar ba a baya.

Ya bayyana haka ne da wata hirar musamman da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce babu wani dan siyasa da zai iya kayar da Shugaba Buhari.

Ya kuma soki tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo, inda ya ce “idan aka ji Obasanjo na maganganu akwai abin da ya nema a gwamnati bai samu ba. Saboda haka ba don Allah yake yi ba,” in ji Gwamna el-Rufai.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai abubuwan da ya kamata a kara gyarawa a gwamnatin Buhari.

Amma ba zai bayyana su ba, saboda a cewarsa ba ya ba da shawara a kafafen yada labarai. Ya ce idan zai ba shugaban shawara zai kebe ne da shi a fadarsa.

Har ila yau ya bayyana daukar Dokta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2019 a matsayin wani yunkuri na ci gaban jihar, ba wai don kawo rabuwar kai a bangaren addini ba.

A bangaren korar malamai ya bayyana cewa mafi yawancin malaman da aka korar a jihar “jahilai ne saboda bai kamata a ce suna aji suna koyarwa ba.”

More News

Lauya ya nemi kotu ta bashi mako 4 ya nemo inda Yahaya Bello ya É“uya

Abdulwahab Mohammed babban lauyan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta bashi makonni huÉ—u domin ya...

ĆŠalibai 9 aka tabbatar da yin garkuwa da su daga jami’an jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa É—alibai 9 aka tabbatar sun É“ace bayan da wasu Ć´an bindiga suka kai farmaki Jami'ar Kimiya da...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Aƙalla mayaƙan Boko Haram biyu ne suka miƙa kansu ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a yankin gabashin jihar Borno. Mayaƙan biyu...

Isa Dogonyaro ĆŠan Majalisar Tarayya Daga Jihar Jigawa Ya Rasu

Isa Dogonyaro wakilin al'ummar ƙananan hukumomin Garki da Baɓura a majalisar wakilai ta tarayya ya rasu. Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin a majalisar tarayya,...