‘Babu mai dauke da coronavirus a Enugu’ | BBC Hausa

Coronavirus

Gwamnatin jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya ta sanar da cewa matar da aka killace ba ta dauke da cutar coronavirus.

An yi wa matar gwajin ne a asibitin Kwararru na Irua da ke jihar ta Enugu bayan da ta dawo Najeriya daga Birtaniya a ciki makon nan.

Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Enugu Dokra Ifeanyi Agujiobi ya fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ya ce cibiyar da ke kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ma ta tabbatar da matar ba ta dauke da kwayar cutar ta covid-19.

Cibiyar da ke kula da cututtuka masu yaduwa, NCDC ta tabbatar sahihancin gwajin bayan ta ita ma ta gudanar da na ta.

NCDC ta wallafa sanarwar ce a shafinta na Twitter:

Matar wadda ‘yar Najeriya ce, ta dawo gida ne daga Birtaniya bayan ta shafe wata biyar a can.

matar ta isa birnin Enugu ne ranar 11 ga wannan watan daga birnin Owerri na jihar Imo domin ta ziyarci dan ta.

Wannan ya kasance karo na farko da aka sami labarin wanda ake tuhuma da kamuwa da cutar coronavirus a yankin kudu maso gabashin Najeriya tun da annobar ta bayyana.

Wannan ne kuma karon farko da aka sami rahoton kan mace, domin kawo yanzu duka rahotanni biyun da aka samu sun shafi maza ne.

Cibiyar NCDC mai aiki domin dakile bazuwar cutar a Najeriya na samun rahotanni irin wannan masu yawa a kowace rana, kuma ta kan tura jami’anta domin su yi gwaje-gwajen da suka dace.

  • Coronavirus ta bulla a kasashen Afirka 26
  • An gano maganin hana coronavirus yaduwa

A ranar Jumma’ar da ta gabata, Ministan Lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya sanar da cewa a cikin wannan makon za a sallami dan kasar Italiyan nan da ya fara shigo da cutar Najeriya bayan ya murmure.

Ya kuma ce za a sallami mutum na biyu da likitoci suka duba lafiyarsa a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar bayan da shi ma aka tabbatar ba ya dauke da cutar.

A ranar Laraba ce dai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana cutar ta Covid-19 a matsayin annobar da ta mamaye dukkan sassan duniya.

More from this stream

Recomended