Babban Sifetan Yan Sanda Ya Kai Ziyara Jihar Filato Mai Fama Da Rikici

Babban Sifetan Yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya ziyarci birnin Jos a ranar Juma’a kan hare haren da aka kai wasu kauyukan jihar a yan kwanakin nan.

Sama da mutane 150 ne aka kashe a wasu garuruwa 17 dake kananan hukumomin Bokkos, Barikin Ladi da kuma Mangu gabanin bikin Kirisimeti.

Gidaje da dama maharan suka kona abun da ya tilastawa mazauna gidajen zama yan gudun hijira.

Biyo bayan faruwar lamarin gwamnatin tarayya ta yi wa mutanen da abun ya shafa alkawarin bin kadin hakkinsu.

A yayin ziyarar, Egbetokun ya gana da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang da kuma sauran masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya kuma bada umarnin gaggawa ga mataimakin babban sifetan yan sanda mai kula da shiya ta 4 da ya tattara ya koma jihar da zama ba tare da bata lokaci.

More from this stream

Recomended