Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil’adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar neman a biya diya ga yaran da aka kama aka tsare sakamako zanga-zangar #Endbadgovernance da suka shiga.

Falana wanda ya na daga cikin lauyoyin waɗanda ake tuhuma da shiga zanga-zangar ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan da shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a saki a yaran.

Yaran na daga cikin mutane 76 da ake tuhuma da laifin cin amanar ƙasa an kuma gurfanar da su gaban babban kotun tarayya dake Abuja inda kotun ta bayar da belinsu kan kuɗi naira miliyan 10 kowannensu.

Biyo bayan koke da fusata da ƴan Najeriya suka yi kan yanayin yunwa da wahala da aka ga  yaran a cikin ya sa shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin sakin su kana ya buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin.

Babban lauyan ya ce za su jira suga matakin da  gwamnati za ta ɗauka tukunna kafin daga bisani su yi magana da waɗanda suke karewa suji mai suke so kafin su gabatar da buƙatar biyan diyyar.

More from this stream

Recomended