Ba za mu iya ci gaba da dakon man fetur ba—ƴan kasuwa

‘Yan kasuwar man fetur sun ce ba za su iya ci gaba da dakon man fetur a fadin kasar nan ba.

Hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dizal da wadannan ‘yan kasuwa ke amfani da shi wajen sarrafa motocinsu.

Yanzu haka ana siyar da shi a kan N1,100 kan kowace lita a wurare da dama.

‘Yan kasuwar sun ce dole ne gwamnatin tarayya ta sa baki cikin gaggawa domin shawo kan lamarin.

Wannan shi ne matsayin ‘yan kasuwa, a karkashin kungiyar masu samar da mai da iskar gas ta Najeriya, NOGASA.

Sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugabansu Benneth Korie ya sanyawa hannu.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...