Ba za mu taɓa sulhu a da ƴan bindiga a Zamfara ba—in ji Gwamna Dauda Lawal

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jaddada alkawarin gwamnatinsa na cewa ba za ta taba yin sulhu da barayi domin samar da zaman lafiya ba.

Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa Malam Mani Mumuni, wanda ya ce gwamnatinsu a shirye take ta yi maraba da duk wata jam’iyyar adawa don neman mafita da kuma kawo karshen rashin tsaro a jihar.

“Ba ni kadai ne Gwamnan PDP ba, amma ni ne Gwamna a Zamfara gaba daya, don haka kowa ya cire wariya daga gwamnatina” Ya kara da cewa hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zabensa nasara ce ga dimokuradiyya da ci gaban al’ummar kasar gaba daya.

Dauda Lawal ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishinsa da ke Gusau, babban birnin jihar.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...