Ba wa Abiy Ahmed kyautar Nobel abun alfahari ne – Buhari

Firaministan Habasha Aby Ahmed

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Firaministan Habasha Aby Ahmed

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce kyautar Nobel ta zaman lafiya da aka karrama firaministan Habasha, Aby Ahmed da ita abin alfahari ne ga Afirka ta yadda firaministan ya iya sasanta rikicin da ke tsakanin kasarsa da makwabciyarta, Eritrea.

A ranar Juma’a ne aka ba Abiy Ahmed kyautar saboda kokarinsa na wanzar da zaman lafiya a tsakanin kasarsa Habasha da makwabciyarta Eritrea da kuma rawar da ya taka wajen sasanta rikicin Sudan tun bayan hawansa karagar mulki.

Shugaba Buhari na Najeriya wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin alfahari ga Afirka baki daya, ya ce shi ma ya cancanci samun kyautar.

Yace kyautar gagarumin ci gaba ne ga nahiyar Afirka ta fuskar zaman lafiya da dorewar kwanciyar hankali.

Sai dai yace Shugaba Buhari ma ya cancanci ya samu wannan kyauta saboda irin rawar da ya taka wajen kawo karshen rikicin al’ummar Tibi da Jukun.

Garba Shehu ya ce dalilin daya sa Najeriya ba ta samun kyautar Nobel din shi ne rashin rubuta kasar da kuma haska irin kokarin da take yi wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

“Mu ba mu roki a ba mu kyautar Nobel ba,” in ji Garba Shehu.

Farfesa Wole Soyinka ne dan Najeriya da ya taba cin kyautar Nobel a 1986, kuma babu wanda ya sake samunta a Najeriya sabanin Afirka ta kudu da mutane da dama suka samu.

Tun bayan da aka bawa Aby Ahmed wannan kyauta ne, shugabannin kasashe da hukumomi suke ta aike sakonnin taya shi murna musamman kan kokarin da yayi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Eritrea a bara bayan kwashe tsawon shekaru ashirin suna takaddama.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueterres ya ce “tsare-tsaren Abiy Ahmed sun taimaka wa Ethiopia da Eritrea wajen kafa tarihin dawo da zaman lafiya”:

Abiy Ahmed dai ya yi wa dubban fursunonin siyasa afuwa, sannan ya bai wa kungiyoyin hamayya da ‘yan jarida damar yin ayyukansu bayan kwashe shekaru ana tauye masu hakki.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Mu ba mu roki a ba mu lambar Nobel ba, amma mun cancanci a ba mu

Kokarinsa na kawo karshen rikicin siyasa a Sudan ya taimaka wajen daukar matakin ba shi wannan kyauta ta Nobel.

Amma wasu sun soki wannan matakin, saboda kamar yadda kwamitin Nobel din ya ce, har yanzu akwai matsalolin da ba a magance ba a Ethiopia.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...