‘Ba matsin da Buhari ke fuskanta kan takararsa’

[ad_1]

Buhari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani game da labarin da wasu jaridun kasar suka wallafa da ke cewa shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba daga manyan kasashen duniya kan ya jingine aniyarsa ta neman wa’adin shugabanci na biyu.

A ranar talata ne Jaridar Daily Independent ta wallafa labarin mai taken Buhari na fuskantar matsim lamba daga manyan kasashen waje.

A cikin labarin an ambaci sunayen kasashe da suka hada da Amurka da Tarayyar Turai da Birtaniya da kuma Saudiyya.

An gina labarin ne daga wasu bayanai da jaridar tace ta samu daga wata babbar majiya a jam’iyyar APC, cewar saboda batun rashin lafiyarsa da fargabar kazancewar rikicin cikin gida na jam’iyyar APC, shugaban ke fuskantar matsim lamba daga kasashen.

Sanarwar da fadan shugaban na Najeriya ta fitar ta ce yana da muhimmaci ta mayar da martani ga labarin wanda jaridar Daily Independent ta wallafa a shafinta na farko ranar talata.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban na Najeriya Femi Adesina, ta ce “Labarin karya ne da ba shi da tushe, wanda wasu makiyan demokuradiya suka yada.”

Sanarwar ta kuma ce sai da shugaba Buhari ya yi dogon nazari kafin sanar da aniyar neman wa’adi na biyu, tana mai cewa wadanda ke tsoron fafatawa da shi ne ke kokarin hana shi tsaya wa ta kara ta ko wace hanya da ya kunshi daukar nauyin wallafa labaran karya a jaridu.

Sanarwar ta kara da cewa wallafa irin wannan labarin abin kunya ne ga jaridar da duk wani da ke son aikin jarida na kwarai.

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...