Ba Coronavirus Ba Ce Ke Kashe Mutane A Kano – Ganduje – AREWA News

A jiya Lahadi Gwamnatin Jihar Kano ta yi ribas kan matsayarta dangane da Yawaitar mutuwa da ake fama da ita a Jihar. Sai dai ta ce, ba Coronavirus ba ce ke kashe Jama’a.

Gwamnatin ta ce tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurci Kwamishinan Lafiya da ya yi bincike mai zurfi kan wannan lamari na Yawaitar mutuwa da musabbabinta.

Matsayar ta Gwamnatin Kano tana kumshe ne a wata takardar manema Labarai da Kwamishinan Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar. Inda ya ce, ana tsaka da yin bincike kan lamarin.

Sai dai ya ce, sakamakon da suka fara samu ya yi nuni da cewa yawaitar mutuwar ba ta da alaka da Coronavirus.

Kwamishinan ya ce, daga rahotannin da suka samu daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar sun yi nuni da cewa mafi yawan matuwar suna aukuwa ne sakamakon hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma zazzabin cizon sauro.

Idan dai ba a manta ba a makon da ya gabata Ganduje ya karyata batun Yawaitar mutuwa a Jihar Kano, Inda ya ce farfagandar makaryata ce kawai.

Related Articles