Auren zumunta na iya jawo cutar kansar ido – Masana

Yadda cutar Kansa take

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Kwararru a fannin lafiya sun ce akwai wani nau’in cutar kansar ido da auren zumunci ke iya kawo shi.

Tsohuwar babbar jami’ar shirin takaita cutar kansa ta Najeriya, Dr. Ramatu Hassan ce ta bayyana hakan a wata hira da BBC Hausa albarkacin Ranar Cutar Kansa Ta Duniya a ranar Talata.

Dr Ramatu ta ce auren zumunci ko na dangi da ake yi tsakanin mutane kan yi sanadin a haifi yaro mai irin wannan lalurar.

Kasashen da ke da yawan auren zumunci kamar arewacin Najeriya na da yawan cutar kamar yadda likitar ta bayyana.

”Irin wannan cuta ta kansar Ido na samuwa ga jarirai tun suna cikin ciki, saboda gado ake yi yawanci, kuma yana faruwa a inda ake yawan yin auren dangi, don haka akwai yiwuwar idan aka ci gaba da auren dangi to kuwa za a ci gaba da samun cutar,” in ji ta.

Cutar na fitowa ne a dai-dai inda ya kamata ido ya gani, sai a haifi yaro da ita a hankali a hankali tana ci gaba da girma, yayin da yaro ya kamata ya fara tafiya sai ya rika tuntube kamar yadda likitar ta bayyana.

Cibiyar yaki da cutar daji ko kansa ta duniya ta ce miliyoyin mutane ne ke cikin hatsarin kamuwa da cutar kansa a rayuwarsu, saboda kawai ba su san hanyar da za su gujewa shiga tarkon cutar ba.

Dr Ramatu Hassan ta ce mutane da yawa a fadin duniya na sakaci da bayanan kare kawunansu daga kamuwa da cutar kansa.

Wasu alkaluma na cewa cutar kansa tana sanadin mutuwar mutum miliyan tara da dubu 600 duk shekara, wato sama da mutanen da ke mutuwa sanadin cutar HIV da Aids da kuma zazzabin cizon sauro da tarin TB.

Kwararru sun yi hasashen cewa nan da shekara ta 2030, mutanen da ke mutuwa duk shekara sakamakon cutar kansa zai karu zuwa miliyan 13.

Likitar ta kuma yi karin bayani kan hanyoyin da za a bi a kare kai daga wannan cuta, “babban matakin da ya kamata a dauka shi ne tun daga farko kafin a yi aure a rika tunnain cewa akwai irin wannan ciwo a dangi ko kuwa,” in ji Dr Ramatu.

More from this stream

Recomended