Auren wuri ‘yana karuwa a Najeriya’

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce auren wuri yana karuwa a Najeriya ne saboda gwamnatin tarayyar da gwamnatocin jihohi ba su dauki wata doka ta hana shi ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen aurar da yara mata da wuri.

Kodayake dokar kare hakkin yara ta 2003 da gwamnatin tarayyar kasar ta yi ta haramta arar da yara ‘yan kasa da shekara 18.

Su kuwa jihohin kasar da ke amfani da tsarin shari’ar musulunci sun gaza amfani da dokar da gwamnatin tarayya ta yi a kan batu aurar da yara ‘yan kasa da shekara 18.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce,” Abin damuwa ne ace kusan shekara 20 da zartar da doka a kasa, amma har yanzu ana aurar da yara mata ‘yan kasa da shekara 18 a kasar”.

More from this stream

Recomended