Atletico Madrid ta koro mai rike da kofin Champions | BBC Hausa

Liverpool

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Liverpool ce ta lashe kofin Champions a 2018/2019

Atletico Madrid ta tsallaka zagayen daf da kusa da na karshe a gasar Champions bayan lallasa Liverpool da ta yi da ci 3 – 2 har gida.

Liverpool dai ita ce ta lashe gasar zakarun Turai a shekarar da ta gabata, amma a bana an kora ta gida a zagayen ‘yan 16.

Georginio Wijnaldum ne ya fara zura kwallo a raga cikin minti na 43 da fara wasan.

Wannan ya bai wa ‘yan wasan Liverpool kwarin gwiwar jin za su iya nasara a wasan lokacin da suke neman kwallo daya domin nasara.

Kwallon da Liverpool ta ci ta sa wasan ya zama kunnen doki saboda kwallo daya ita ma aka zura mata a wasan da suka na Spaniya.

Bayn cikar minti 90 ne a wasan, sai aka yi karin lokacin minti 30 domin samun gwani.

Roberto Firmino ne ya fara jefa kwallo a raga cikin karin lokacin da aka yi a minti na 90+4.

Dan wasan Atletico Madrid Marcos Llorente ne ya farke mata duka kwallaye biyun da aka zura mata a minti na 90+7 da kuma minti na 105.

A daidai lokacin Liverpool ta fito neman kwallo kwanta-da-kwarkwatarta abin da ya bai wa Alvaro Morata damar tamfatsa kwallo ta uku a ragar LIverpool.

Yanzu dai damar Champions ta kubuce wa Liverpool, ko da yake tana wata dama a gaba cikin gasar Premier inda kawai take bukatar wasa biyu domin lashe ta.

More from this stream

Recomended