Atiku ya ziyarci Wike

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda jam’iyar PDP ta tsayar a matsayin dantakarar ta a zaben 2023 ya ziyarci gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a gidansa dake Abuja.

Wike shi ne wanda yazo na biyu a zaben fitar da gwani da jam’iyar PDP ta gudanar ranar Asabar a Abuja.

A cikin wani sako da ya wallafa a soshiyal midiya Atiku ya ce ya kai ziyarar ne domin ganin cewa an tafi tare da kowa a inuwar jam’iyar PDP.

More from this stream

Recomended