Atiku ya ziyarci mutanen da suka jikkata a hatsarin motar jihar Filato

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP,Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci mutanen da suka jikkata a hatsarin motar da ya faru a jihar Filato.

Atiku tare da rakiyar wasu jiga-jigan jam’iyar PDP sun ziyarci mutanen ne dake samun kulawar likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Jos JUTH.

Har ila yau Atiku ya dakatar da yakin neman zabensa a ranar Lahadi domin jimamin abin da ya faru.

Mutane 16 ne yan jam’iyyar PDP da suka fito daga karamar hukumar Pankshin suka mutu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar su ta zuwa yakin neman zabe.

More from this stream

Recomended