Atiku Ya Shilla Zuwa Kasashen Turai

Dantakarar shugaban kasa a jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi balaguro zuwa kasashen Turai.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da ya kaddamar da kunshin mutanen da za su jagoranci yakin neman zaben sa.

Mr Paul Ibe mai bashi shawara kan kafafen yada labarai a cikin wata sanawa da ya fitar ya ce tafiyar ta Atiku bata da alaka da batun ganin likita domin a duba shi kamar yadda wasu suke yadawa.

“Da yammacin yau Atiku zai ta fi kasashen Turai domin kasuwanci” A cewar Ibe.

Har ila yau ya ce Atiku zai biya Dubai domin ganawa da wasu daga cikin iyalansa.

More News

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da motoci masu amfani da iskar gas ta CNG

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin shugaban kasa na samar da motoci masu amfani da iskar gas ta CNG. Shirin an samar da shi...

NDLEA ta kama wani mai safarar miyagun kwayoyi

Hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kama wani É—an kasuwa, Sherif Egbo mai shekaru 40 a filin...

An kai wa gwamnan Kogi hari

Gwamnatin jihar Kogi ta ce jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kashe gwamnan jihar Yahaya Bello a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga...

Gwamnatin Najeriya za ta biya alawus É—in N-Power na wata tara

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara biyan bashin watanni tara ga masu cin gajiyar shirin N-Power da ke shirin farawa daga watan Nuwamba....