Atiku Ya Shilla Zuwa Kasashen Turai

Dantakarar shugaban kasa a jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi balaguro zuwa kasashen Turai.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da ya kaddamar da kunshin mutanen da za su jagoranci yakin neman zaben sa.

Mr Paul Ibe mai bashi shawara kan kafafen yada labarai a cikin wata sanawa da ya fitar ya ce tafiyar ta Atiku bata da alaka da batun ganin likita domin a duba shi kamar yadda wasu suke yadawa.

“Da yammacin yau Atiku zai ta fi kasashen Turai domin kasuwanci” A cewar Ibe.

Har ila yau ya ce Atiku zai biya Dubai domin ganawa da wasu daga cikin iyalansa.

More from this stream

Recomended