Dubban magoya bayan jam’iyar PDP ne suka halarci taron gangamin da jam’iyar ta shirya a shiyar arewa maso gabas.
Taron na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ya samu halartar dan takarar shugaban kasa a jam’iyar Alhaji Atiku Abubakar da kuma mataimakinsa Ifeanyi Okowa.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya bayyana murnarsa kan dandazon taron mutanen da ya gani a wurin.