Atiku ya lashen zaben fitar da gwani na PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa,Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani da na takarar shugaban kasa da jam’iyar PDP ta gudanar a birnin tarayya Abuja.

Atiku ya lashe zaben ne da kuri’u 371 inda gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike yazo na uku da kuri’u 237 tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki shi ne mutumin da yazo na hudu da kuri’u 70 sai gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel yazo na hudu da kuri’u 38.

A jawabinsa na murnar lashe zaben da yayi, Atiku yayi alƙawarin haɗakan al’umma sake ginawa da kuma ciyar da kasa gaba.

More from this stream

Recomended