Atiku ya karɓi ɓakuncin wasu manyan ƴan siyasa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya karbi bakuncin iyalan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai a gidansa dake unguwar Asokoro a Abuja.

Makasudin ziyarar ta su shi ne neman auren ƴarsa, A’isha Atiku  Abubakar.

A cikin manyan baƙin da suke cikin tawagar akwai mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido da na jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

More from this stream

Recomended