Shugaban jam’iyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gana da Alhaji Mujahid Dokubo Asari shugaban kungiyar ceto al’ummar yankin Niger Delta.
Dokubo ya taya Ganduje murnar zaben sa da aka yi a matsayin sabon shugaban jam’iyar APC.
A wani sako da aka wallafa a shafin X wanda a baya ake kira Twitter jam’iyar APC ta ce ganawar ta gudana ne a gidan Ganduje dake Abuja.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da aka fitar kan dalilin ganawar mutanen biyu.