Tauraron dan wasan Ghana Asamoah Gyan ya sauya ra’ayi game da yin ritaya daga taka wa kasarsa leda bayan shugaban kasar ya bukace shi da ya dawo.
Dan wasan mai shekara 33, wanda ya zura kwallo 51 a wasa 106 ya bayyana cewa ya yi ritaya ne a ranar Litinin bayan sauya shi a matsayin kaftin din tawagar kasar.
Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya yi magana da shi a ranar Talata, abin da ya sa dan wasan gaban kungiyar Kayserispor din ya lashe amansa.
“Bai kamata a ki mutunta bukatar shugaban kasa ba,” in ji shi.
“Na karbi bukatar da zuciya daya kuma zan bayar da hadin kai ga kocimmu Kwasi Appiah.
A ranar Laraba ake sa ran Ghana za ta bayyana sunayen ‘yan tawagar da za su wakilce ta a gasar cin Kofin Kasashen Afirka da za yi a kasar Masar.
Ana kuma sa ran Andre Ayew ne zai rike kaftin din kungiyar.
Gyan bai buga wa Ghana wasa ba tun Saptambar 2017 bisa rauni da ya sha fama da shi, kuma ba ya samun buga wa kulob dinsa na Kayserispor wasa a-kai-a-kai.
Ya bayyana cewa hankoronsa na taimaka wa Ghana lashe kofin Afirka “yana da girma sosai” kuma “zai yi bakin kokarinsa wajen hidimta wa al’umma da kasa baki daya”.
Asamoah Gyan ya zura kwallaye a wasannin karshen Kofin Afirka guda shida a jere hadi da gasar cin Kofin Duniya daga shekarun 2006 zuwa 2014.