Arsenal na zawarcin David Luiz daga Chelsea | sport news

David Luiz celebrates with Olivier Giroud

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

David Luiz ya buga wasa sama da 150 a gasar Firimiya a Chelsea

Dan wasan baya na Chelsea, David Luiz, na daya daga cikin ‘yan kwallon da Arsenal ke nema domin karfafa bangaren baya na kungiyar.

Luiz, wanda kwantiraginsa zai kare a shekarar 2021, bai yi atisayi da tawagar manyan ‘yan kwallon kungiyar ba a ranar Laraba.

Dan wasan mai shekara 32 ya halarci atisayen a Cobham kuma bai bijirewa wani umarni ba – amma dai ba a yi komai da shi ba.

Arsenal za ta fara kakar Firimiya ta bana a Newcastle ranar Lahadi, yayin da Chelsea za ta ziyarci Manchester United.

More from this stream

Recomended