APC ta lashe zaben gwamnan Bayelsa, na Kogi ‘bai kammalu ba’ | BBC Hausa

0
Zauren da aka bayana sakamakon zaben gwamnan Bayelsa
Image caption

Zauren da aka bayana sakamakon zaben gwamnan Bayelsa

Hukumar zabe a jihar Bayelsa ta bayyana David Lyon na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.

Mr Lyon ya samu kuri’u 352,552 da suka ba shi damar doke sauran yan takara da suka hada da Mista Duoye Diri na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu da kuri’u 143,172.

To amma Mista Diri dai ya yi fatali da sakamakon tun ma a lokacin da ake tattara shi.

Yadda ta kaya a jihar Kogi

A jihar Kogi hukumar zaben ta ce zaben Sanata da akayi a Kogi ta Yamma bai kammalu ba, kasancewar kuri’un da aka soke sunfi yawan wadanda wanda ke kan gaba ya bada tazara.

Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ke kan gaba da kuri’u 80,118, yayin da mai bin sa Dino Melaye na jam’iyyar PDP ke da kuri’u 59,548.

To sai dai tun kafin bayyan sakamakon Mista Melaye yayi watsi da sakamakon da ake tattarawa.

A yanzu hukumar ta ce za ta saka lokacin da za ta gudanar da zaben cike gibi.

A wata mai kama da haka kungiyoyin da ke sa ido kan zaben sun yi watsi da sakamakon da aka tattara na zaben gwamna da sanata, inda suka ce an tabka kura-kurai.

An dai samu rikici a zaben jihar ta Kogi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku ranar Asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here