APC ta kira taron gaggawa da gwamnonin jam’iyar

Gabanin zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya na ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya kira wani taron gaggawa na gwamnonin jam’iyar.

Taron da aka shirya yin sa da karfe 2 na ranar Lahadi ne na zuwa ne kasa da mako guda kafin fara zabukan 2023.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan makasudin taron amma jaridar Vanguard ta gano cewa baya rasa nasaba da abubuwan da suke faruwa da suka haɗa da karancin kuɗi da kuma tasirin da hakan yake da shi a lokutan zabe.

More from this stream

Recomended