
Jam’iyar APC ta dage taron shugabanninta da kuma na kwamitin zartarwar jam’iyar.
Abubakar Kyari, shugaban rikon jam’iyar shi ne ya fadawa manema labarai haka bayan wani taron gaggawa na shugabannin jam’iyar na kasa a ranar Litinin.
Taron shugabannin da aka yi a hedikwatar jam’iyar dake Abuja an kira shi ne biyo bayan murabus ɗin shugabanta, Abdullahi Adamu da kuma sakataren jam’iyar, Iyiola Omisore.
Kyari ya ce canjin shugabanci da aka samu a jam’iyar shi ne dalilin dage taron.
Shugaban rikon jam’iyar ya ce nan gaba kadan za a sanar da ranar taron.