10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaAnnobar cutar kwalara ta kashe mutane 7 a Jigawa

Annobar cutar kwalara ta kashe mutane 7 a Jigawa

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

An samu ɓarkewar annobar cutar kwalara a ƙaramar hukumar Kirikasamma da kewayenta a jihar Jigawa.

Kawo yanzu mutane 7 aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyar annobar a yayin a wasu da dama ke can kwance a asibiti inda suke karbar magani.

Jami’in tsare-tsare na hukumar kula da lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Kirikasamma, Musa Abdullahi Digadige ya ce ɓarkewar annobar cutar ta shafi ƙauyuka da dama da suka haɗa da Malori, Maikintari, Dilmari, Kirikasamma, da kuma wani sashe na na ƙauyen Baturiya.

A cewar Digadige alamomin cutar sun haɗa da gudawa,  ƙullewar ciki, jin yin amai, amai da kuma zazzaɓi.

Shugaban Sashen Ruwa da Tsafta, Muhammad Maisamari ya ce an tura tawagar jami’an kiwon lafiya ya zuwa yankunan da abun ya shafa domin su bayar da kulawar  da ta kamata.

Ƙaramar hukumar ta kuma sayo magunguna da sauran kayayyakin da suka kamata domin samun nasarar maganin cutar.

Daraktan mulki da gudanarwa na ƙaramar hukumar, Idris Gambo Abubakar ya yi alƙawarin bayar da dukkanin taimakon da ya dace domin daƙile yaɗuwar cutar.

Hukumomi sun alaƙanta ɓarkewar cutar da gurɓatar ruwan sha sanadiyar ambaliyar ruwa da aka samu a yankin sanadiyyar mamakon ruwan sama.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories