
Hakkin mallakar hoto
EPA
Cutar Coronavirus na iya shafar rayuwar mutane a fannin da ba na lafiya ba. Saurin yaduwar da cutar ke yi, ya sa kamfanonin sufurin jiragen sama dakatar da jigilarsu zuwa China, inda cutar ta fara bulla.
Kamfanin jirage na Kenya Airways ya sanar da dakatar da jigilar fasinjoji har sai nan gaba, haka ma kamfanonin jirage na RwandAir da Air Madagascar da Air Mauritus da sauransu.
Masana tattalin arziki dai na ganin cewa wannan zai haifar da nakasu a tattalin arzikin Afrika da na China da ma duniya baki daya.
Farfesa Muhammad Muttaka Usman, wani masani kan harkar tattalin arziki da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ya ce rashin zirga-zirga tsakanin nahiyar da China zai takaita kasuwanci.
“Kasashen Afrika da dama sun ta’allaka a China da samun abubuwan amfani don haka idan jiragen nahiyar suka soke zuwa to lallai wannan zai shafi kasuwanci da tattalin arzikinsu,” a cewarsa.
Farfesa Muttaka ya ce kawo yanzu barkewar cutar Coronavirus ta jawo wa China asarar kusan dala miliyan 60, don haka “dole zai shafi tattalin arzikin duniya.”
Ya ce zai yi wuya tattalin arzikin kasashen Afrika ya iya ci gaba ba tare da kasuwanci da China ba.
Ranar Alhamis ne Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ayyana cutar coronavirus a matsayin babbar barazar lafiya a duniya.
Kawo yanzu cutar ta kashe sama da mutane 300 a China kuma tana ci gaba da yaduwa inda hukumomin China suka tabbatar da cewa an sake gano wasu mutum dubu biyu sun kamu da cutar.
Kasashe da dama sun rufe iyakokinsu daga baki masu zuwa daga China, yayin da jami’ai ke aiki don shawo kan yaduwar cutar.
Amurka da Australiya sun ce za su hana duka bakin da suka je China kwanan nan biza.
Kasashe kamar Rasha da Japan da Pakistan sun sanar da irin wadannan sabbin dokoki da suka sa don dakile yaduwar coronavirus.