Ana zargin wani mutumi da yin lalata da ƴar shekara 4

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Delta, Wale Abass ya bayar da umarnin janye karar lalata da wani dalibi dan shekara hudu da wani mutum mai shekaru 46 ya yi daga kotu domin gudanar da bincike mai kyau.

Da yake magana a madadin Kwamishinan ƴan sanda, mai magana da yawun rundunar, DSP Bright Edafe, ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a ranar Asabar a Asaba.

Ya ce, “Rundunar ta na sane da wani labari da aka buga a kafafen sada zumunta daban-daban kan zargin lalata da wani Innocent Ezeukwu, mai shekaru 46, mai kula da makarantar Great Leader International School ya yi da yarinya ƴar shekara huɗu.

“A ranar 5 ga Oktoba, 2023, wata Misis Joy Chukwudi ta ruwaito cewa yayin da take wankan ‘yarta ‘yar shekara hudu, ta gano wani tabon jini a gaban ‘yarta.”

“Kwamandan yankin Agbor ya yi karin bayani kan tawagar masu binciken da za su ci gaba da zuwa wurin wanda ake zargi da aikata laifin kuma an kama wanda ake zargin Innocent Ezeukwu.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...