Ana zargin wani mutumi da hallaka tsohuwar matarsa

Wani mutum da aka bayyana sunansa a matsayin Muftau Adefalu ana zargin ya kashe tsohuwar matarsa, Yetunde Olayiwole, a yankin Sango-Ota na jihar Ogun.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta bayyana wa manema labarai cewa an kama wanda ake zargin kuma yana tsare bayan rasuwar Olayiwole.

Kakakin rundunar, Omolola Odutola, ta bayyana  da yammacin Asabar cewa lamarin ya faru da misalin karfe 8:00 na dare ranar Juma’a, 1 ga Nuwamba, 2024.

Ana zargin cewa wanda ake zargin mai shekara 37 ya samu sabani da matar, wanda ya haifar da rikici a tsakaninsu.

Odutola ta ce, “Mutumin ya samu sabani da tsohuwar matarsa wanda ya kai ga rikici. Ta fadi har kasa a lokacin da ake tsaka da rikicin kuma aka garzaya da ita asibiti don samun taimakon likita.

“Daga baya likita ya tabbatar da rasuwarta. An kai gawarta dakin ajiye gawa na Asibitin Ifo domin binciken likitanci. An kama wanda ake zargi kuma yana tsare.”

More from this stream

Recomended