Connect with us

Hausa

Ana gwabza yaki a Syria | BBC news

Published

on

AFP

Hakkin mallakar hoto
AFP

Ana gwabza yaki kusa da garin Ras al-Ain na Syria da ke kan iyakar kasar tsakanin mayakan Kurdawa da kuma sojojin Turkiyya.

Turkiyya ta bayyana cewa ta kwace iko da garin amma mayakan Kurdawa na SDF sun musanta hakan.

Kasar ta Turkiyya ta musanta kai hari ga sojojin Amurka bayan shelkwatar tsaron Amurkar ta bayyana cewa an kai hari ga dakarunta da ke yammaci.

Rahotanni sun bayyana cewa a kalla an kashe fararen hula 30 kuma sama da mutum 200,000 sun rasa muhallansu a cikin kwanaki hudu.

Matakin da Shugaba Trump ya dauka na janye dakarun Amurka daga yankin ya yi sanadiyar kara harzuka harin da Turkiyya ta kai wa mayakan Kurdawa.

Turkiyyar dai ta zargi Kurdawa da ”ta’addanci” inda ta ce tana so ta tasa keyarsu daga inda take so ta kafa sansaninta a cikin Syria domin shirinta na tsugunar da ‘yan gudun hijirar Turkiyya a kasar kusan miliyan uku.

Mayakan Kurdawa na cikin kawayen Amurka na yaki da ‘yan kungiyar IS.

Wani babban kalubale da kasashen duniya ke fuskanta shi ne makomar dubban fursunonin yaki na kungiyar IS da suke hannun mayakan Kurdawa da ke yankin.

A cikin makon nan dai Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto inda ta bayyana cewa a kalla mutane 100,000 ne suka yi kaura daga gidajensu a arewacin Syria sakamakon hare-haren Turkiyya a yankunan da ke hannun mayakan Kurdawa.

Rahotannin Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutanen na zama ne a makarantu da wasu gine-gine.

Facebook Comments

Hausa

Jiragen Birtaniya za su koma sauka Sharm el-Sheikh | BBC news

Published

on

The plane was on its way to St Petersburg when it crashed

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Jirgin na ka hanyarsa ta zuwa St. Petersburg ne a lokacin da bam ya tashi

Birtaniya za ta mayar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasarat da yankin shakatawa na Sharm el Sheikh mai farin jini na kasar Masar.

Kusan shekara hudu da ta gabata aka soke dukkan zirga-zirga zuwa can saboda wani harin bam da aka kai kan wani jirgin sama na Rasha.

Kungiyar IS ce ta dauki alhakin kai harin, wanda yayi sandiyyar mutuwar fiye da mutum 200.

Wani gagarumin sakaci a filin jirgin saman Sharm el Sheikh shekara hudu da ta ganata ne ya bayar da kafar da wasu suka dasa wani bam a cikin jirgin saman Rasha da ke kan hanyarsa ta komawa birnin St. Petersburg.

Dukkan wadanda ke cikin jirgin su 224 wanda samfurin Airbus ne sun rasa rayukansu a lokacin da bam din ya tashi yayin da jirgin ke sararin samaniya.

Birtaniya ce kan gaba wajen dakatar da dukkan jiragen kasarta da sauka a filin na Sharm el Sheikh, matakin da ya fusata gwamnatin Masar.

Kasar ta yi fargabar matakin zai shafi tattalin arzikinta da ya ta’allaka kan yawan bude idanu, musamman daga kasashen yammacin Turai.

Amma sauran kasashe ma sun dauki irin wannan matakin.

Masana harkokin tsaro a yankin sun yi itifakin cewa wasu magoya bayan kungiyar IS ne suka dasa bam a jirgin Rashar…

An shafe shekara hudu kafin Birtaniya ta amince ta kyale jiragenta komawa can, kuma kamfanonin masu harkokin yawon bude idanu sun ce suna duba yiwuwar ci gaba da ba mutane karfin gwuiwar ziyartar Sharm el Sheikh.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Abba Kyari ya kama masu garkuwa da mutane 81 da ke addabar titin Abuja-Kaduna – AREWA News

Published

on

Hazikin ‘Dan sanda DCP Abba Kyari Sarkin Yaki, dodon masu garkuwa da mutane, babban kwamandan rundinar ‘yan sanda kwararru na IGP-IRT ya samu nasaran farautar wasu gungun masu garkuwa da mutane da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja, da kuma masu aikata miyagun laifuka a cikin garin Abuja da kewaye, da kuma wasu daga jihar Taraba

A cikin wadanda aka kama akwai manyan yaran Shu’aibu Dan Kaduna, kuma sune suka addabi hanyan Kaduna da Abuja, amma shi Shu’aibu ya rasa ransa a wani artabu tsakaninsa da ‘yan sanda kwanaki kadan da suka gabata.

Wasu daga cikin wadannan da aka kama kuma sune suka kashe Jami’an ‘yan sanda Inspector Patrick Yuhana da wasu ‘yan sanda a watan August da ya gabata, tsakanin hanyar Abuja da Kaduna, sai kuma ‘yan dafara ta yanar gizo guda goma (10), wato “Internet fraudsters, harda ‘dan kasar Ghana a cikinsu.

Ansami bindigogi kirar AK47 guda takwas (8) da harsashi guda dari uku da arba’in da bakwai (347), da wasu manyan makamai guda 15, Computer guda goma (10), da zunzurutun kudi naira million goma (N10,000,000) wanda suke karba kudin fansa a hannun wadanda suke kamawa.

‘Yan ta’adda kun shiga uku wallahi!, duk ‘dan da yace uwarsa ba zatayi bacci ba, to shima ba zaiyi bacci ba, babu gurbin buya ga masu aikata miyagun laifuka a Nigeria da iznin Allah Jinjina ga DSP Maibindiga, ASP Abdurrahman Muhammad Ejily da sauran dakarun IRT

Muna rokon Allah Ya tsare mana DCP Abba Kyari tare da jama’arsa, Allah Ka kara musu nasaran da tafi wannan. Amin.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Sojoji ‘sun tursasa wa wasu ‘yan Kenya iyo a ruwan ba-haya’

Published

on

Ruwan kwata

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu ‘yan kasar Kenya sun shiga shafin Twitter don bayyana fushinsu kan wani rahoton da wata jaridar kasar, Standard Newspaper, ta wallafa cewa wasu sojoji sun ci zarafin wasu mazauna birnin Mombasa da ke bakin ruwa, a ranar Lahadi a lokacin da ake bukukuwan ranar gwarzaye.

An tsaurara matakan tsaro a birnin, a yayin da kasar ke bukukuwan wanda shugaban kasar, Uhuru Kenyatta, da wasu manyan kusoshin gwamnati suka halarta.

Jaridar ta wallafa rahoton da ke cewa an tursasa wa wasu mazauna birnin yin ninkaya a cikin ruwan ba-haya, yayin da kuma aka tursasa wa wasu zama a cikin tabo.

Wasu kuwa mazauna yankin sun yi zamansu ne a gida, saboda tsoron ka da sojoji su muzantasu, a cewar rahoton.

Sai dai kawo yanzu sojojin ba su ce komai ba game da zarge-zargen.

Wani matashi mai shekara 23 a duniya wanda ake kira Chikore, ya shaida wa jaridar cewa, yana kan hanyarsa ce ta zuwa wajen taron bikin lokacin da sojoji suka tsayar da shi saboda basu yarda da shi ba.

“Sun yi kokawa da ni har suka kaini kasa, daga nan kuma suka sa na yi iyo a cikin ruwan ba-haya. Na yi kokarin gudu amma sai suka buga mini gindin bindiga,” In ji shi.

Masu mu’amala da shafin Twitter sun bayyana wannan lamarin da cewa “abin kunya ne” kuma “abin kyama”:

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited