Ana Gardama Kan Cancantar Gina Jami’ar Sufuri a Daura

Kwararru a fannin ilimi sun nuna cewa gina irin wanan Jami’ar da za ta koya wa matasa yadda za su sarrafa ababen hawa musamman ma jiragen kasa, da yanzu ake amfani da shi, abu ne mai alfanu a kasa kuma zai ba matasa damar dogaro da kansu duk da cewa ana cikin wani yanayi na raguwar tattalin arziki. Farfesa Sani Sambo na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria yana cikin masu wanan tunanin inda ya ce a duk lokacinda aka ce Jami’a za a yi to abu ne da ya kamata yan kasa su yi na’am da ita ba wai a yi ta suka akai ba domin matasa da ke fama da rashin aikin yi za su amfana kuma a haka kasa ce za ta amfana.

To sai dai ga daya daga cikin Dattawan Arewa Dr. Usman Bugaje gina Jami’ar a Daura bai dace ba, domin a kwanan nan aka kafa wata Makarantan Kimiya da fasaha a Daura, saboda haka wanan abu bambadanci ne kawai mutane ke yi, kuma shugaban Kasa ake so a burge kuma yin haka rashin adalci ne. Bugaje ya ce sannu a hankali ma za a ce sai shugaban Kasa ne zai za6i shuwagabanin Jami’ar kuma haka zai kawo rashin jituwa.

Amma wani kwararre a fannin ilimi na bai daya, Hassan Sardauna Hammayo yana ganin yin wanan Jami’a a yanzu ya dace domin babu irin ta a kasa baki daya, kuma za a samu kwararru daga jami’ar wadanda za su habbaka fannin sufuri.

Shi kuwa mai nazari kan al’amuran yau da kullum, Abubakar Aliyu Umar ya ce ba kyauta ba ne, wannan ai cin fuska aka yi wa ‘yan kasa domin za a sa mutane cikin yanayin bauta ne kawai ga kasar China. Aliyu ya ce inda Shugaba Buharin da ya sani ada ne, da ya ce kar a kai Jami’ar Daura, saboda kar a ga kamar yana da hannu a ciki.

Abubakar Aliyu ya ce an yi rashin adalci saboda jami’o’in da ake da su yanzu suna neman rugujewa saboda rashin kula. Ya ce me zai hana a habba Cibiyar Koyar da dabarun sufuri da ke Zaria idan har ana so a samu cigaba mai dorewa?

Wanan Jami’a da Kamfanin CCECC ta Kasar China ke ginawa a kyauta za ta lakume kudi har dalar Amurka miliyan 50.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...