Ana fargabar mutuwar mutane da dama a wani ginin bene da  ya ruguzo kan mutane a jihar Legas

Wani ginin bene mai hawa biyu da ake aikin ginawa a yankin Ikotun dake Lekki a jihar Legas ya ruguzo da daren ranar Talata.

Mutane biyu maza biyu aka tabbatar da sun mutu a yayin da jami’an aikin ceto ke cewa akwai yiwuwar akwai karin mutane dake cikin baraguzan ginin.

Ibrahim Farinloye jami’in tsare-tsare na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA a jihar Lagos ya ce kawo yanzu ba a san dalilin faduwar ginin ba.

Ya ce hukumar ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa a cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar.

” Da isar jami’ai wurin sun iske ginin bene mai hawa biyu ne da ake ginawa ya ruguzo ,”a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa mutane biyar aka ceto dukkansu na ɗauke da munanan raunuka kuma tuni aka kai su asibiti.

Itama hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos ta ce tana cigaba da gudanar da aikin ceto a wurin.

More from this stream

Recomended