Connect with us

Arewa

Ana ci gaba da zanga-zanga a rana ta uku a Legabon

Published

on

Masu zanga-zangar a kusa da ginin majalisar kasar rika sun jefawa 'yan sanda wuta, da duwatsu

Bayanan hoto,
Masu zanga-zangar a kusa da ginin majalisar kasar rika sun jefawa ‘yan sanda wuta, da duwatsu

A rana ta uku a jere, a na cigaba da arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a Beirut babban birnin Lebanon, yayin da jama’a ke nuna fushinsu a kan fashewar nan da ta janyo rasa rayukan fiye da mutane 200.

Zanga-zangar ta ci gaba duk da murabus din da gwamnati ta yi a ranar Litinin, inda mutane da yawa ke zargin ministocin da sakaci.

Masu zanga-zanga a kusa da ginin majalisar kasar rika sun jefawa ‘yan sanda wuta, da duwatsu da abubuwan fashewa, yayin da ‘yan sandan ke maida martani da gurneti da kuma barkonon tsohuwa.

Da yake sanar da murabus dinsa Firai ministan kasar, Hassan Diab, ya nisanta kansa da alhakin fashewar, ya kuma ce shirye-shiryensa na kawo sauyi ne ga tsarin siyasar kasar da aka gurbata.

Ko da a kwanan baya, kasar ta yi fama da mummunan rikicin tattalin arzikin kasar.

Bayanan hoto,
Fira ministan kasar, Hassan Diab,

Mene ne sanadin fashewar ?

Shugaban Lebanon Michel Aoun ya ɗora alhakin fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate da aka jibge cikin wani ɗakin ajiyar kaya na tashar jirgin ruwan birnin.

A shekarar 2013, wani jirgin ruwa mai suna MV Rhosus yayi jigilar sinadarin. Bayan ya yada zango a tashar jirgin ruwa na Beirut saboda wata matsalar inji a kan hanyarsa daga ƙasar Georgia zuwa Mozambique, sai hukumomin tashar suka hana shi barin tashar bayan sun binciki kayan da yake ɗauke da su.

Kamar yadda shafin intanet na Shiparrested.com ya ruwaito, masu jirgin ruwan sun yi watsi da lamarin jirgin ruwan nasu a tashar, lamarin da yasa aka kwashe sinadarin daga ciki zuwa wani ɗakin ajiya mai lamba 12 bayan wata kotu ta bayar da umarnin yin haka.

Tun wancan lokacin sinadarin ke jibge cikin ɗakin, maimakon a sayar da shi ko dai a raba shi da wurin.

Shugaba Aoun ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan fashewar.

“Mun ƙuduri niyyar ci gaba da bincike kuma za mu bayyana yadda wannan abin takaicin ya auku ba tare da jinkiri ba, kuma duk wadanda aka samu da sakaci da ya janyo fashewar za su ɗandana kuɗarsu,” inji shugaban ranar Laraba bayan ya zaga cikin tashar jirgin ruwan.

Firai minista Hassan Diab ya bayyana yadda aka bari fasewar ta auku “abin da ba za a amince da shi ba.”

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending