Ana ceto mutane da kwale-kwale ya kifa da su a Kebbi

Kwale-kwale ya kifa inda ake kyautata zaton cewa mutanen ciki sun nitse a ruwa a lokacin da suka sami hatsari a Yauri da ke jihar Kebbi.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda ake danganta hatsarin sakamakon rashin kyawun yanayi da mamakon ruwan sama a kogin Niger da ya ratsa jihar Kebbi.

Wani ganau, Haruna Rafin Kuka Yauri, ya ce ana can ana ci gaba da duba gawawwakin mutanen da suka rasu.

Ya ce ba su kai ga gano adadin mutanen da suke cikin jirgin ba.

Shugaban karamar hukumar ta Yauri, Bala Muhammad Gagga, ya ce an zakulo gawawwaki huÉ—u zuwa yanzu.

More News

Lauya ya nemi kotu ta bashi mako 4 ya nemo inda Yahaya Bello ya É“uya

Abdulwahab Mohammed babban lauyan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta bashi makonni huÉ—u domin ya...

ĆŠalibai 9 aka tabbatar da yin garkuwa da su daga jami’an jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa É—alibai 9 aka tabbatar sun É“ace bayan da wasu Ć´an bindiga suka kai farmaki Jami'ar Kimiya da...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Aƙalla mayaƙan Boko Haram biyu ne suka miƙa kansu ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a yankin gabashin jihar Borno. Mayaƙan biyu...

Isa Dogonyaro ĆŠan Majalisar Tarayya Daga Jihar Jigawa Ya Rasu

Isa Dogonyaro wakilin al'ummar ƙananan hukumomin Garki da Baɓura a majalisar wakilai ta tarayya ya rasu. Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin a majalisar tarayya,...