Fadar shugaban Najeriya ta ce ana amfani da kananan jirage da kuma masu saukar ungulu wajen kai wa ‘yan bindiga makamai a dazukan da ke yankunan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fadi hakan a wata hira da BBC Hausa, inda yake kare sabon matakin da gwamnati ta dauka na hana giftawar jiragen sama ta cikin jihar.
A jiya Talata ne gwamnatin Najeriya ta ce ta ɗauki ƙarin matakai a jihar Zamfara ciki har da haramta haƙar ma’adanai da kuma hana giftawar jiragen sama ta cikin jihar.
Malam Garba Shehu ya ce: “Akwai rahotanni da ake samu ba wai a jihar Zamfara ba har wasu sassan na arewacin Najeriya, jirage masu saukar ungula da wasu masu hakar ma’adinai kan yi amfani da su, ana zargin cewa a kan dauki makamai a kai daji wajen ‘yan ta’adda.
“Kuma sannan ana amfani da wadannan jirage a debi gwal da ake haka a wasu sassan Zamfara a tafi da su kasar waje. Wannan magana ta yi karfi domin har a yanzu da ake magana, a Dubai akwai kasuwa ta gwal din Najeriya.
“Gwamnati na asara, jama’ar kasar nan na asara, shi ya sa aka ce an dakatar da hakar gwal din nan ga wanda duk ba gwamnati ta sa shi ya yi ba.
Malam Garba ya kara da cewa an bai wa jami’an tsaro umarnin daukar mataki kan duk wani jirgi da aka ga yana shawagi a wannan yanki.
Ba wannan ne karo na farko da aka hana hakar gwal ba a Zamfara amma hakan bai yi tasiri ba, don Malam Garba ya ce maganar gaskiya ita ce ba a daina ba.
“Hakar gwal din iri biyu ne, akwai masu lasisi da izini, akwai masu bugar kirji suna yi ba tare da izini ba, saboda suna ganin sun isa za su iya zama kariya ko hani su shiga su yi wadannan abubuwa,” in ji shi.
Ana amfani da wadannan jirage a debi gwal da ake haƙa a wasu sassan Zamfara a tafi da su ƙasar waje. Domin a yanzu da ake magana,akwai kasuwa ta gwal din Najeriya a Dubai.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce shi ya sa gwamnati ta sake daukar wannan matakin saboda fitinar satar mutanen, maimakon ana ganin an shawo kanta sai karuwa take.
“To idan har akwai gudunmowa da wannan fitina ke samu wajen hakar gwal da ake da kuma wadannan jirage da ke shiga da fita wadannan yankuna, to gwamnati ta ce a dakata,” a cewar Malam Garba.
Sai dai akwai wani batu mai sarkakiya na ta yadda za a gane mahakan gwal masu lasisi da marasa lasisi, amma Garba Shehu ya ce gwamnati ta san matakin da za ta bi.
“Wanda aka ba shi izini dai an ba shi. Wannan lamari ba ‘yan Najeriya kadai ke shiga cikinsa ba.
“Akwai mutanen da musamman daga kasar waje ma suke shigowa su kebe waje su samu sansani su debi arzikin da Allah Ya ba mu su gudu da shi, kuma su taimaka wajen wannan fitina da ake yi wajen kawo makamai ga mugayen mutane da ke wadannan dazuzzuka.
Malam Garba ya jaddada cewa gwamnati ba za ta bari a ci gaba da yin wadannan mugayen abubuwa ba.
Mene ne matakin?
A ranar Talata ne gwamnatin Najeriya ta ce ta ɗauki ƙarin matakai a jihar Zamfara ciki har da haramta haƙar ma’adanai da kuma hana giftawar jiragen sama ta cikin jihar.
Sakamakon yadda ake fakewa da harkar hakar ma’adonin, ana kara rura wutar matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar da ma yankin arewa maso yammacin Najeriyar.
Matakin na zuwa ne bayan wani taron majalisar tsaron ƙasa da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Muhammadu Buhari.
Haka zalika, shugaban ya kuma umarci ministan tsaron ƙasar da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro su tura ƙarin sojoji masu yawa zuwa yankin da nufin shawo kan taɓarɓarewar tsaron da ake fama da ita.
Me ake nufi da hana giftawar jiragen sama ta Zamfara?
Mutane da dama za su yi mamaki me ya hada jihar Zamfara da a hana jirgin sama bi tun da ba ta da filin sauka da tashin jiragen.
Wani mai sharhi kan al’amuran tsaro, Group Kaftin Sadiq Garba Shehu mai ritaya ya ce matakin hana giftawar jiragen sama ta jihar Zamfara “No Fly Zone”, wata dabara ce da ake amfani da ita idan ana yakin kasa, inda kasar da ke da karfi amma tana ga abokiyar gabarta na da karfin sojin sama, sai ta kakaba mata wannan doka, cewa ta hana jiragen soja yin zirga-zirga a yankin.
Ya ce a tarihi, Majalisar Dinkin Duniya ke bai wa kasashe damar kakabawa. Abu biyu ke sa a irin wannan matakin kamar yadda masanin ya ce.
“Na farko idan yaki ne wanda ya hada da fararen hula da ake gallaza musu ta sama, to don a kare fararen hular sai MDD sai ta bai wa kasashe damar kakaba wannan matakin don hana jirage shawagi ta wannan waje,
Group Kaftin Sadiq ya ce an fi amfani da kalmar “No Fly Zone” a inda ake yaki, kuma wata kasa ce ke kakaba wa wata kasa. Shi ya sa ni a fahimtata yin amfani da wannan kalmar a wannan yanayi na Zamfara bai zo a daidai ba.
Ya kara da cewa a saninsa na sha’anin soji bai san wadannan maharan suna da karfin soja ba, “don a sha’anin soja kowace kalma ka yi amfani da ita tana da ma’anarta.
Matakin jirage mai saukar ungulu kawai ya shafa ko har da na fasinja na cikin gida da ketare?
Ya ce ana sanya dokar “No Fly Zone” ne a kan jiragen soja na abokan gaba ba a kan dukkan jirage ba. Sauran jiragen fasinja ko na masu kai dauki ana ba su damar sauka.
Karin labarai masu alaka
To ko wanne irin tabarbarewar tsaro ne zai sa a dauki matakin “No Fly Zone”?
A ganin Group Kaftin Sadiq al’amarin na so ya gagari kundila, “saboda idan ana ta sa matakai ba sa aiki sai lamarin ya zama kamar ya fi karfin gwamnati.”
Ya ce akwai daga cikin abubuwan da ka iya faruwa da jiragen da hanya ta bi da su ta jihar zamfara, kamar misali ana iya sa wani jirgin ya sa wancan dole ya sauko kasa.
Sannan idan ta baci ana ma iya harbo jirgin.
“Gaskiya wannan mataki ba zai yi wani tasiri ba, da kamar a ce ‘yan ta’addan na da jirgin sama irin nasu da suke kai hari to a nan “No Fly Zone” zai yi amfani.
“Labarin cewa masu hakar gwal na zuwa a jirage babu tabbas a cikinsa kuma wannan ma ba za a iya amfani da kalmar “No Fly Zone” ba,” a ganin masanin.