10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaAn yi jana'izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin da tayi na yi masa bikin binnewa na musamman.

Akinkumi wanda ya mutu ranar 4 ga watan Satumba na shekarar 2023 yana da shekaru 87 ya kamata ace an girmama shi da jana’iza ta ban girma daga gwamnatin tarayya amma iyalansa suka gaji da jira abun da ya sa suka gudanar da bikin binne shi.

Akinwunmi Akinkumi ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin ya ce iyalan sun yi hakuri sun jira suga ko gwamnatin tarayya za ta cika alƙawarin da ta ɗauka amma shiru.

Ya bayyana cewa a ƙullum suna biya naira ₦2000 kuɗin ajiyar gawar a ɗakin ajiye gawarwaki.

Gwamnatin jihar Oyo ita ɗauki nauyin bikin binne marigayin da aka fara ranar Laraba aka kuma kammala ranar Juma’a a Ibadan babban birnin jihar.

An haife shi a ranar 10 ga watan Mayu a shekarar 1936 a garin Ibadan, Akinkumi an sanshi da wanda ya ƙirƙiri tutar Najeriya a shekarar 1958 inda aka bashi kyautar fam 100 a wancan lokaci.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories