An tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da ceto wasu 30 a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Kogin Niger da ke kusa da Mmiata Anam a karamar hukumar Anambra ta Yamma a jihar Anambra.
An tattaro cewa kwale-kwalen yana tafiya ne daga jihar Kogi zuwa Anambra ta kogin Niger kafin ya kife a gabar kogin Mmiata.
Wata majiya a yankin Riverine na al’ummar ta shaida cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi.
Wani faifan bidiyo da aka yi ya nuna cewa waɗanda suka mutu mata ne da yara.