Rahotanni sun nuna mutane 6 sun mutu yayin da 11 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kaduna zuwa Zariya.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Kaduna, Kabir Nadabo, ya ce hatsarin ya afku ne a tashar Aliko da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata da misalin karfe 06:25 na safe.
Nadabo ya alakanta yawaitar haɗurran da suka yi da yin tukin ganganci, lamarin da ya janyo dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wani dan lokaci.
Sai dai ya ce hanyar a halin yanzu babu walwala da zirga-zirga, inda ya ce tawagar masu aikin ceto na Zebra 35 Rigachikun sun kai dauki cikin gaggawa inda suka kai dauki.