An yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa, Dauda Adamu da aka fi sani da Rarara.

Rahotanni sun nuna cewa an yi awon-gaba da Hajiya Adamu bulala daga gidanta da ke kauyen Kahutu, da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina.

Zuwa yanzu dai ba a ji komai daga bakin mawakin ba.

More from this stream

Recomended