An Yi Ca Akan Jaridar Sahara Reporters

VOA Hausa

Jaridar Sahara Reporters ta yanar gizo na fuskantar kakkausan suka a shafukan sada zumunta musamman ma a Twitter bayan da ta wallafa wani labari da ke cewa shugaban kungiyar izala a Najeriya Sheikh Bala Lau ya rasu.

Sai dai shugaban ya fito ya musanta lamarin a cikin wani faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta.

“Mai kokarin cewa zai wallafa labarin mutuwar wani, idan ya yi hakuri sai ta Allah ta kasance a kan sa.”

“Ni lafiya ta kalau kuma ban san me ya sa suka rubuta wannan labarin ba.”

Wannan al’amari na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta Izala ta yi rashin babban malaminta Sheikh Adamu Gashua a jihar Yobe.

A lokacin da Sahara Reporters ta fitar da sanarwar cewa shugaban ya rasu, sun kuma wallafa wasu hotuna inda suka yi ikrarin cewa jana’izar shugaban ne.

Bayan da bidiyon shugaban ya fito, sai suka goge labarin, suka sake wallafa wani sabon labari mai cewa shugaban na nan da rai.

Tuni dai ‘yan Twitter suka yi ta furta kalamai marasa dadi akan jaridar ta Sahara da kuma saka alamar tambaya kan manufar wallafa labarin.

Matasa da dama sun umarci shugaban da ya kai jaridar kotu bisa yadda lamarin ya bata musu rai.

Sai dai shugaban bai ce uffan ba tun bayan da ya aka saki bidiyon nasa.

A cikin ‘yan kwannakin nan jaridar na yawan fuskantar suka bisa sahihancin labaran da take wallafawa.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...