Wasu rukunin matasa sun fantsama kan tituna a ranar Juma’a inda suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hukuncin kotun ƙoli da ya tabbatar da zaɓen, Abdullahi Sule a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.
Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa masu zanga-zangar sun ƙona tayoyi a gaban ginin ofishin jam’iyar PDP dake Lafiya.
Har ila yau masu zanga-zangar sun ƙona tayoyi akan babbar hanyar tafiya birnin Jos babban birnin jihar Filato.
Zanga-zangar ta jawo an rufe makarantu dama wuraren sana’a a birnin na Lafiya.
Tushen Abin Da Ya Faru
Biyo bayan ƙarar da ɗan takarar jam’iyar PDP a zaɓen gwamnan jihar, David Ombugadu ya shigar kotun sauraren kararrakin zaɓe ta tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar.
Gwamna Sule ya ɗaukaka ƙarar hukuncin inda kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar masa da nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da aka yi.
Rashin gamsuwa da hukuncin kotun ɗaukaka karar ne ya sa Ombugadu ya ɗaukaka ƙara ya zuwa kotun ƙoli inda kuma a yau ta yanke hukuncin da ya bawa gwamna Sule nasara.