An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan gyaran hali da tarbiyya na Suleja dake jihar Niger.

A ranar 24 ga watan Afrilu wani mamakon ruwan sama ya rushe wani sashe na katangar gidan gyaran hali na Suleja har ta kai ga É—aurarru 118 sun tsere.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya É—ora alhakin rushewar katangar kan tsufa da tayi.

Inda ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da kare faruwar haka anan gaba.

Ƴan kwanakin da suka wuce, Abubakar Umar mai magana da yawun hukumar ta NCoS ya ce an samu nasarar kama 23 daga cikin fursunonin da suka tsere.

Ya zuwa ranar 15 ga watan Yuni hukumar ta wallafa sunayen mutanen da suka tsere a shafin intanet na hukumar.

Sunayen da aka wallafa sun haÉ—a da Ogbonna Kingsley, Auwal Mohammed, Mustapha Ibrahim, Suleiman Sani, Raphael Kelly, Abdullahi Babangida, Idris Bashir, Umar Mustapha, Ayuba Obedience, da Lamido Gambo.

Sauran su ne Garba Fidelis, Mohammed Jibrin, Sylvester Allison, Albert Israel, Edoga Okwudili, Olaiya Stephen, Ibrahim Aminu, da Audo Usman.

More News

Shan giya na halaka sama da mutum miliyan 2.6 duk shekara—WHO

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya nuna cewar shan giya na kashe mutum miliyan 2.6 a duk shekara. Rahoton ya ƙara da cewa...

Ƴan fashin daji sun kashe ƴan bijilante 4 da ɗan sanda ɗaya a Kaduna

Wasu da ake zargin ƴan fashin daji ne sun kai farmaki mazaɓar Kakangi dake ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe...

Ƴan Boko Haram sun yi garkuwa da wani alƙali da matarsa a jihar Borno

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da alƙalin babbar kotu mai Shari'a, Haruna Mshelia tare da matarsa da kuma dogarinsa. Rahotanni sun bayyana cewa...

Abdul Aziz Yari ya dauki nauyin karatun dalibai 1,700 a Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya baiwa 'yan asalin jihar 1,700 tallafin karatu a...