An tura wani mutum gidan yari bayan da ya ɗirkawa yarinya  ƴar shekara 11 ciki

Wata kotun majistire dake Ikeja a jihar Lagos ta tasa keyar Muyiwa Shonibare mai shekaru 42 ya zuwa gidan yari bayan da aka zarge shi da yin lalata tare da yiwa wata yarinya ƴar shekara 11 ciki.

Alƙaliyar kotun mai shari’a,E. Kubeinje ta umarci jami’an ƴan sanda da su miƙa takardun ƙarar ofishin babban mai shigar da ƙara na jihar domin ya bada shawararsa kana ta dage shari’ar ya zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.

Tun da farko ƴan sanda na tuhumar Shonibare wanda yake zaune a layin Odeyele a unguwar Agode Egbe dake yankin Ikotun  a jihar ta Lagos da laifin fyaɗe.

Mai gabatar da ƙara, SP Kehinde Ajayi ya faɗawa kotun cewa Shonibare ya aikata laifin tsakanin watan Agusta zuwa Nuwamban shekarar 2023.

Related Articles